19/08/2026
Gomnatin Gwamna Babagana Umara Zulum ta bayyana cewa ta zuba jarin ₦15.29bn a fannin tallafin karatu na ɗaliban jihar tun shekarar 2023, inda aka karkata sama da ₦8.61bn wajen ɗaukar dawainiyar karatun ƙasashen waje.
Gwamna Zulum ya sanar da hakan ne a taron maraba da ɗalibai 294 da s**a kammala karatunsu na ƙasashen waje a China, India, Egypt da Malaysia. Haka zalika, ya amince da fitar da kudi kimanin ₦2.65bn domin biya wa ɗalibai 158 da ke kan karatu bashin shekarar 2026.
Rarraban kudin tallafin ya kasu kamar haka:
₦8.61bn: Dawainiyar karatun ƙasashen waje.
₦3.83bn: Tallafin karatun ɗaliban cikin gida.
₦196.3m: Ayyukan gudanarwa na hukumar tallafin karatu.
Gwamnan ya jaddada cewa haɓaka ilimin matasa shi ne hanya mafi tabbas ta yaƙi da talauci da kangarar tsaro. Tare da hakan, ya sanar da ƙara adadin kudin tallafin karatu na ɗaliban cikin gida da kashi 100% (100 percent increase), inda ya umarci Kwamishinan Ilimi da Hukumar Scholarship da su aiwatar da hakan nan take.
Kwamishinan Ilimi, Engr. Lawan Abba Wakilbe, ya ƙara da cewa tsarin na kasashen waje ya maida hankali ne kan fannonin likitanci da injiniyari, kuma ɗalibai 171 sun kammala karatun digiri na biyu da na uku daga kasashen India da Malaysia guda 16 daga cikinsu da sakamako mai ninkayyar kyautatuwa (distinction).