18/03/2026
𝒀𝒂𝒘𝒂𝒏𝒄𝒊𝒏 𝒎𝒖𝒕𝒂𝒏𝒆 𝒔𝒖𝒏𝒂 𝒛𝒂𝒓𝒈𝒊𝒏 𝒓𝒂𝒔𝒉𝒊𝒏 𝒔𝒂’𝒂 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒂𝒌𝒂 𝒉𝒂𝒏𝒂𝒔𝒖 𝑽𝒊𝒔𝒂… amma gaskiya ba haka bane. Dalili shine 𝐰𝐚𝐭𝐬𝐢 da waɗannan sharuɗɗan a yayin neman 𝐕𝐢𝐬𝐚𝐫.
𝐄𝐦𝐛𝐚𝐬𝐬𝐲 𝐛𝐚𝐬𝐚 𝐠𝐲𝐚𝐫𝐚 𝐦𝐚𝐤𝐚 𝐤𝐮𝐬𝐤𝐮𝐫𝐞. Kada kuji tsoro ayau zamuyi magana akan ƙananan Dalilai guda 𝟑 dake kawo hanuwar samun Visa (𝑉𝑖𝑠𝑎 𝑅𝑒𝑗𝑒𝑐𝑡𝑖𝑜𝑛), kuma zamuyi bayani a kansu dalla-dalla domin ku guje musu.
1. 𝐍𝐚 𝐟𝐚𝐫𝐤𝐨. 𝑲𝒂 𝒕𝒂𝒃𝒃𝒂𝒕𝒂𝒓 𝒅𝒂 𝒕𝒂𝒌𝒂𝒓𝒅𝒖𝒏𝒌𝒂 𝒔𝒖𝒏 𝒄𝒊𝒌𝒂: Nasan zakuyi mamakin yadda wasu, koma na kusa da ku, ke fama wajen neman Visa wata da watanni, wasu lokutan ma har shekara da shekaru. Babban muhimmin abu da embassy suke dubawa shine 𝐜𝐢𝐤𝐚𝐤𝐤𝐢𝐲𝐚𝐫 𝐡𝐮𝐣𝐣𝐚𝐫 𝐝𝐚𝐰𝐨𝐰𝐚 𝐍𝐢𝐠𝐞𝐫𝐢𝐚 𝐚 𝐫𝐮𝐛𝐮𝐜𝐞.
𝐼𝑑𝑎𝑛 𝑘𝑎𝑖 𝑚𝑎’𝑎𝑖𝑘𝑎𝑐𝑖𝑛 𝑔𝑤𝑎𝑚𝑛𝑎𝑡𝑖 𝑛𝑒 (civil servant), ka tabbatar ka aje Employment letter ko kuma takardar Contract da kamfanin da kake aiki.
𝐺𝑎 𝑑𝑎𝑛 𝑘𝑎𝑠𝑢𝑤𝑎, embassy suna duba takardar shaidar rajistar sana’a wato (𝐂𝐀𝐂).
𝐼𝑑𝑎𝑛 𝑡𝑎𝑓𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑔𝑎𝑦𝑦𝑎𝑡𝑎 𝑐𝑒, auratayya, taro, ko samun aiki, ka gamsar da su da cikakkiyar shaida a rubuce wadda ke nuna niyyar tafiyarka.
𝐺𝑎 ɗ𝑎𝑙𝑖𝑏𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎, ka nuna hujjar takardar barin makaranta kai tsaye daga makarantar (𝐒𝐜𝐡𝐨𝐨𝐥 𝐥𝐞𝐚𝐯𝐞 𝐚𝐩𝐩𝐫𝐨𝐯𝐚𝐥).
Sannan kuma ana mantawa da 𝗯𝗮𝗻𝗸 𝘀𝘁𝗮𝘁𝗲𝗺𝗲𝗻𝘁, musamman idan embassy s**a lura da manyan kuɗi da aka saka lokaci ɗaya ba tare da tsohon transaction da ke nuna makamancin kuɗin ba. 𝑾𝙖𝒏𝙣𝒂𝙣 𝙨𝒉𝙞 𝙣𝒆 𝒃𝙖𝒃𝙗𝒂𝙣 𝙖𝒃𝙞𝒏 𝒅𝙖 𝙠𝒆 𝒌𝙖𝒘𝙤 𝙬𝒂𝙨𝒊-𝒘𝙖𝒔𝙞 𝙖 𝙜𝒂𝙧𝒆𝙨𝒖.
2. 𝑵𝒂 𝒃𝒊𝒚𝒖. 𝑻𝒂𝒃𝒃𝒂𝒕𝒂𝒓 𝒃𝒂𝒚𝒂𝒏𝒂𝒏𝒌𝒂 𝒔𝒖𝒏 𝒚𝒊 𝒅𝒂𝒊𝒅𝒂𝒊:
Ka gama haɗa takardu kuma ka shirya zuwa interview… amma shin bayananka sun yi daidai?
Duk abin da ka rubuta a takardunka, ka tabbatar ya dace da abin da zaka fada a interview.
Misali, idan ka rubuta kwanaki 14 zakayi, sai ka ce kwanaki 20 a interview — wannan yana kawo shakku.
Kada ka fada wani abu daban da baka rubuta ba. Kada ka ƙirƙira dogon labari, sannan kuma kada ka yi gajeren bayani da zai sa su yawaita tambayoyi saboda rashin fahimta. 😅
3. 𝑵𝒂 𝒖𝒌𝒖. 𝑲𝒂 𝒃𝒂𝒚𝒚𝒂𝒏𝒂 𝒅𝒂𝒍𝒊𝒍𝒂𝒏 𝒕𝒂𝒇𝒊𝒚𝒂𝒓𝒌𝒂:
Ba kawai “ 𝐼𝑛𝑎 𝑑𝑎 𝑏𝑢𝑘𝑎𝑡𝑎𝑟 𝑡𝑎𝑓𝑖𝑦𝑎” ba.
Ka tabbatar da cewa dalilan tafiyarka yana da cikakkiyar shaida wadda tazo daidai da hujjojin da ka gabatar a application ɗinka.
𝐊𝐚 𝐲𝐢 𝐦𝐚𝐠𝐚𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐤𝐰𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐠𝐰𝐢𝐰𝐚 💪, 𝐤𝐚 𝐟𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐛𝐢𝐧 𝐝𝐚 𝐤𝐚 𝐫𝐮𝐛𝐮𝐭𝐚 𝐚 𝐭𝐚𝐤𝐚𝐫𝐝𝐮𝐧𝐤𝐚, 𝐬𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐤𝐚𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐜𝐨𝐩𝐲 𝐧𝐚 𝐇𝐨𝐭𝐞𝐥 𝐛𝐨𝐨𝐤𝐢𝐧𝐠 𝐝𝐚 𝐅𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭 𝐈𝐭𝐢𝐧𝐞𝐫𝐚𝐫𝐲 𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐧𝐮.
TOP Comments
L’Aviatrice Travel