Inside Katsina State

Inside Katsina State The heartbeat of Katsina state news Domin kawo sahihan Labarai Da Rahotanni Daga Birni, Karkara Da Sassan Jihar Katsina. Mun gode.

Haka nan kuma, za mu rika kawo labarun da suka shafi Tarihi, Wasanni, Addinai da duk wani abin da ya shafi fadakarwa, Tunatarwa, Wa'azantar, Ankararwa, Nuni, har ma kuma nishadantarwa daga ko'ina a fadin duniya. Sai dai, ya danganta da dacewar lokacin dora maku shi ko kawo maku shi a wannan saha tamu.

APC Ta Tsayar Da AB Dabai A Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Ta Bakori Da Danja Jam’iyyar APC ta tsayar da AB Daba...
16/05/2026

APC Ta Tsayar Da AB Dabai A Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Ta Bakori Da Danja

Jam’iyyar APC ta tsayar da AB Dabai a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakori da Danja, bayan cimma matsayar sulhu tsakanin masu neman tikitin jam’iyyar.
An tabbatar da hakan ne bayan sauran masu neman takarar sun janye domin bai wa AB Dabai damar zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027 mai zuwa.
Rahotanni sun ce an gudanar da tsarin tabbatar da zaɓen ne bisa tanadin doka tare da sa ido daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki.
Jam’iyyar ta yaba wa masu neman takarar da s**a amince da matsayar da aka cimma, tana mai cewa matakin zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mambobinta.
APC ta kuma yi kira ga dukkanin ’ya’yanta da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓe mai zuwa.
Daga cikin waɗanda jam’iyyar ta yaba wa gudunmawarsu akwai Yakubu Nuhu Danja da Yusuf Muhammad Jika da kuma Shehu Dabo Dabai.
Jam’iyyar ta yi musu fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya ba AB Dabai nasara a zaɓen da ke tafe.

Kungiyar PDP a Matazu Ta Bukaci Babba Mazoji Ya Sake Tsayawa TakaraWata kungiyar wayar da kan jama’a mai alaka da jam’iy...
29/04/2026

Kungiyar PDP a Matazu Ta Bukaci Babba Mazoji Ya Sake Tsayawa Takara

Wata kungiyar wayar da kan jama’a mai alaka da jam’iyyar PDP a karamar hukumar Matazu ta bukaci Hon. Zarahaddeen “Babba Mazoji” da ya sake tsayawa takara a zaben da ke tafe, bisa abin da ta bayyana a matsayin gudunmawar alheri da ya bayar a baya.

Kungiyar, wadda ke karkashin sunan PDP Political Awareness Movement Matazu, ta bayyana cewa Babba Mazoji ya gudanar da ayyukan jin kai da dama a lokacin da yake neman takarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina a shekarar 2023.

A cewar kungiyar, gudunmawar da aka bayar ta shafi bangarori daban-daban da s**a hada da ilimi, lafiya, tsaro da walwalar al’umma, wanda a cewarsu ya taimaka wajen inganta rayuwar jama’a a yankin.

“Mun ga irin ayyukan alheri da ya gudanar, don haka muke kira gare shi da ya sake fitowa takara a kowace jam’iyya domin ci gaba da tallafa wa al’umma,” in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar.

Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran ‘yan takara a yankin da su fito da irin gudunmawar da s**a bayar ga al’umma, domin bai wa jama’a damar tantance nagartarsu.

Ta jaddada cewa siyasa bai kamata ta zama ta cin mutunci ko zagin juna ba, sai dai a mayar da hankali wajen bayyana ayyukan alheri da shirye-shiryen da za su amfani al’umma.

A karshe, kungiyar ta yi addu’ar Allah Ya zaba wa al’ummar Matazu shugabanni nagari masu kishin ci gaban jama’a.

28/04/2026

Malam Ayuba Gambarawa ya zargi shirin cusa dan takarar majalisar tarayya a Katsina ta tsakiya wanda ba shi al'umma ke so ba

Katsina Law Firm Petitions Govt Over Hisbah Raid, Missing ₦221mA Katsina-based legal firm, Legal Minded Law Firm, has pe...
27/03/2026

Katsina Law Firm Petitions Govt Over Hisbah Raid, Missing ₦221m

A Katsina-based legal firm, Legal Minded Law Firm, has petitioned the state government over alleged misconduct by operatives of the Katsina State Hisbah Board, including claims of unlawful invasion, harassment, and the disappearance of ₦221 million.

The petition, dated March 18, 2026, was addressed to Governor Dikko Umaru Radda on behalf of a businessman, Alhaji Jibrin Tanimu.

According to the firm’s lawyers, D. D. Sani and I. M. Sa’ad, the incident occurred in the early hours of March 10, when about 25 Hisbah operatives allegedly stormed the client’s residence.

The operatives, reportedly led by Nafi’u Akilu, were said to have forced entry into the premises around 1:20 a.m., damaging the gate and windows and causing panic among occupants.

The lawyers alleged that the operatives continued banging on doors and moving around the compound until the businessman surrendered.

They further claimed that after gaining access to the client’s bedroom, a sum of ₦221 million kept in the house went missing and has yet to be recovered.

Following the incident, the businessman was reportedly taken around Katsina for several hours before being detained at the Hisbah office along Jibia Road. His lawyers said he was initially denied access to his phone and legal representation.

The petition also stated that the arrest was linked to an ongoing case before Upper Sharia Court II in Katsina. Despite obtaining and serving a court order on a Hisbah official identified as Muhammadu Sh*tu, the legal team alleged that the order was ignored.

The businessman was later transferred to Kano State, where he remained in custody until he was granted bail on March 16, 2026.

Legal Minded Law Firm described the incident as a violation of fundamental rights and due process, urging the state government to investigate the actions of the Hisbah operatives.

However, the Hisbah authorities denied the allegations.

Muhammadu Sh*tu, the DCS Operations who led the operation, said the petitioner had been on a wanted list for allegedly defrauding individuals through fake job offers, from which he reportedly collected over ₦10 million in Kano.

He dismissed claims of unlawful invasion and theft, questioning the credibility of the allegation that ₦221 million was kept in the residence.

Sh*tu added that if such an amount existed, it would warrant investigation by the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC).

Speaking on behalf of the Hisbah Commander, Dr. Aminu Usman, he maintained that the agency acted on a valid police arrest warrant and only visited the premises to effect the arrest, insisting that operatives did not enter the petitioner’s living quarters.

Address

Abuja

Telephone

+2348061364011

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Inside Katsina State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Inside Katsina State:

Shortcuts

Share