13/05/2026
Ba kudi ba ne kadai yake kawo daraja.
Akwai dabi'u 10 da suke sa a girmama namiji a duk inda ya shiga.
1. Cika alkawari.
Namijin da maganarsa bata zama aiki... darajarsa zubewa take a idon mutane a hankali. Babu wanda zai fada masa, amma kowa zai daina yadda da shi.
2. Sarrafa zuciyarka.
Musamman fushi. Darajarka tana gushewa a daidai ranar da mutane s**a gane yadda zasu tayar maka da hankali cikin sauki.
3. Yin aiki a sirrance.
Duk yadda ka cika surutu akan abinda kake son yi... haka darajar nasarar take raguwa idan ta fito. Koyi aiki a shiru.
4. Tsari a harkar kudi.
A zahirin gaskiyar duniya... girmamawa tana bin namijin da aljihunsa yake da tsari ne.
5. Tsaya akan tsari.
Idan baka da tsari ko doka akan rayuwarka... mutane zasu dauko tasu dokar su dora a kanka.
6. Girmama kowa, amma kar kaji tsoron kowa.
Asalin karfi... nutsuwa ne. Hayaniya rauni ne a boye.
7. Daukar alhaki.
Namijin da yake yawan dora laifin kasawarsa akan wani, a tsaye yake. Baya taba cigaba.
8. Cigaba da gina kanka.
Asalin girmanka, shine kokarin da kake yi na gyara kura-kuranka a boye.
9. Kare nutsuwarka.
Namijin da kowa zai iya jefa shi a rudani, baya zama abin dogaro.
10. Tafiya da alkibla.
Namijin da ya san inda ya dosa... kowa yana bashi hanya ya wuce.
Fushi. Gajiya. Rudani. Koyi hadiye su a gaban mutane.
Ba wai don baka da zuciya ba.
Sai dai Saboda duniya tana kallon yadda kake daukar matsi ne kafin ta baka girma.
Koyi nutsuwa a lokacin da komai yake a cabe maka.
Yana sa ka zama mai hatsari.
UMAR ALIYU DAHIRU