
14/08/2025
Bayani akan Kungiyar Taimakon Al'umma.
Gabatarwa
Za ka iya Tura Gudummawarka ta wannan Asusun Kungiya.
Association Name: DHM COMMUNITY SUPPORT.
Account Number: 0235396762.
Bank: UNION BANK OF NIGERIA.
DHM COMMUNITY SUPPORT ƙungiya ce mai zaman kanta wadda aka kafa domin kula da walwalar al’umma da kuma kawo musu sauƙin rayuwa. Manufar ƙungiyar ita ce ta zama haske ga marasa galihu da yankunan da aka manta da su, ta hanyar gina rayuwa mai ma’ana da dorewa.
Manufa (Vision)
Muna so mu zama jagorori wajen raya al’umma, ta hanyar kare mutuncin jama’a, tabbatar da walwala, da samar da ci gaba mai ɗorewa ga kowa da kowa.
Ayyukan da za muyi (Mission)
Gina gidaje masu sauƙi ga marasa galihu.
Samar da ruwan sha ta hanyar tono rijiyoyi da boreholes.
Gina da gyara makarantu, masallatai, da cibiyoyin lafiya.
Shirya horo da koyar da sana’o’in dogaro da kai ga matasa da mata.
Daukar nauyin karatun marayu da yaran da ba su da galihu.
Samar da tsaro ga al’umma ta hanyar tura masu gadin tsaro inda ake fama da matsalolin tsaro.
Rabawa jama’a kayan agaji: abinci, tufafi, da magunguna.
Wadanda za su Amfana da wannan Kungiyar.
Marayu da yara marasa gata.
Zawarawa da iyalai marasa galihu.
Matasan da ke neman abin dogaro.
Mutanen karkara da aka manta da su.
Masu bukata a asibitoci da makarantu.
Ƙudurinmu
Kungiyar DHM COMMUNITY SUPPORT ta ɗauki alƙawarin kasancewa garkuwa ga jama’a daga talauci, rashin ilimi, rashin lafiya da rashin tsaro. Mun kuduri aniyar kawo sauyi ta hanyar haɗin kai da kuma ci gaba da ayyukan jinƙai.
Za ka iya tura Gudummawarka ta wannan Asusun
Association Name: DHM COMMUNITY SUPPORT.
Account Number: 0235396762.
Bank: UNION BANK OF NIGERIA.
Kuyi shafe saboda Jama'a su amfana.